Dangane da matsalar, kamfanin da ya mallaki tashar na Tokyo Electric Power ya sanar a ranar 3 ga wata da cewa, an ci tura a matakin da aka dauka na neman toshe tsagar bango da kankare, don haka yanzu ana kokarin zuba wani sinadarin da zai kumbura idan ya hadu da ruwa a cikin na'urar da nufin katse malalewar ruwa mai bulbushin nukiliya.
A sa'i daya kuma, ma'aikatan kamfanin na kokarin kwashe ruwa daga gindin na'urar sarrafa makamashin nukiliya, ta yadda za a sanya ma'aikata shiga ciki, su farfado da injuna masu sanyaya na'urar. (Bello Wang)