in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar kawancen kasashen Afrika ta goyi bayan madatsar ruwa ta Inca da Kongo Kinshasa ta kafa
2012-02-06 15:14:54 cri

Kwanan baya, jami'in ma'aikatar kula da harkokin makamashi ta kasar Kongo Kinshasa ya nuna cewa, gwamnatin kasar na shirin kafa wata madatsar ruwa a Inca, aikin da ya sami goyon baya daga kungiyar tarayyar kasashen Afrika (AU).

Bayan kammala wannan aiki, zai taimaka wajen samar da wutar lantarki a nahiyar Afrika gaba daya, wanda zai taimaka sosai wajen magance matsalar karancin wutar lantarki a wasu kasashen Afrika. Bisa tsarin da kungiyar AU ta yi na samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da karfin ruwa kafin shekarar 2020, a cikin shekaru 8 masu zuwa, kasashen Afrika za su kara karfin bunkasa sabbin makamashi ciki har da makamashi na bola jari, karfin hasken rana da madatsar ruwa ta Inca da sauransu. Ya zuwa shekarar 2020, wadannan sabbin makamashi za su samar da wutar lantarki kilo waz milyan 10.

An ba da labari cewa, madatsar ruwa ta Inca tana jihar Kongo dake yankin karshen kogin Kongo, wadda za ta iya samar da wutar lantarkin da ya kai kilo waz miliyan 44.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China