in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 15 sun mutu, 90 sun samu rauni a sabbin hare-hare a Iraki
2013-05-22 10:48:38 cri

'Yan sanda sun bayyana cewa, a kalla mutane 15 ne suka mutu, kana guda 90 sun samu rauni sakamakon hare-hare a kasar Iraki ranar Talata.

Wani bom ya tashi a cikin mota kusa da babban masallacin Abu Ghraib, wanda masallcin 'yan Sunni ne a unguwar Ghraib, mai nisan kilomita 25 da birnin Bagadaza, ranar Talata da yamma, inda ya yi sanadin rayukan mutane 8, kana 15 suka samu rauni, bisa labari da wata majiya da ba ta son a san ko waye ta bayyanawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua. Fashewar ta lalata motocin farar hula da gine-gine.

A kuma wannan rana, an kashe sojojin Iraki guda uku, kana 7 sun samu rauni a wani harin da wasu 'yan bindiga suka kai cibiyar soji ta Tarmiya mai nisan kilomita 30 daga birnin Bagadaza, in ji 'yan sanda.

A halin da ake ciki kuma an kashe mutane 3, kana 43 sun samu rauni bayan tashin bama-bamai a motoci a unguwar Hussein a garin Tuz Khormato mai nisan kilomita 170 daga birnin Bagadaza.

Hakazalika an kashe farar hula daya, kana 25 sun samu rauni bayan tashin bom bi da bi a kasuwar raguna ta Auraba a gundumar Kirkuk mai nisan kilomita 250 daga birnin Baghdad.

Tashin bama-baman ranar Talata ya biyo bayan sake barkewar tashin hankali tsakanin 'yan Sunni da 'yan Shi'a, wanda ya yi kamari tun bayan janyewar dakarun Amurka daga kasar a karshen shekarar 2011.

A ranar Litinin, harin bama-bamai da harbe-harbe a fadin kasar Iraki ya yi sanadin rayukan mutane a kalla 70, ciki har da masu ziyara 'yan kasar Iran, yayin da sama da 200 suka samu rauni, wanda ake ganin wani sabon yunkuri ne na cusa kiyayya tsakanin 'yan kasar Iraki.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China