in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wajibi ne a hukunta wadanda suka kai hare-hare a Kabul, in ji kwamitin sulhu na MDD
2013-05-27 10:16:48 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya jaddada bukatar da ke akwai ta hukunta wadanda suka kai hare-haren ta'addaci a Kabul, babban birnin Afghanistan a ranar Jumma'a, kana ya nanata kudurinsa na yaki da duk wani nau'in ayyukan ta'addaci.

A cikin wata sanarwa da kwamitin mai mambobi 15 ya bayar, mambobin sun kuma nanata matukar damuwarsu dangane da irin barazanar da Taliban, Al-Qaida da haramtattun kungiyoyi masu dauke da makamai ke haddasa wa ga mazauna yankin, dakarun tsaron kasar, sojojin kasa da kasa da kuma tallafin kasa da kasa da ake bayarwa a kasar ta Afghanistan.

A ranar Jumma'a da yamma ne wasu 'yan bindida dadi masu yawa da 'yan kunar bakin wake suka kai hare-hare a wurare da dama, ciki har da harabar hukumar kula da harkokin shige da fice ta kasa da kasa(IOM) da ofishin 'yan sanda da ke tsakiyar Kabul, lamarin da ya yi sanadiyar raunana ma'aikatan hukumar guda 3, kuma kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare, tana mai zargin cewa, wurin da ta kai harin, gidan hutawan sojoji ne.

Mambobin kwamitin sulhun sun kuma nuna juyayi tare da mika ta'aziya ga iyalan wadanda lamarin ya shafa da kuma gwamnatin da al'ummar Afghanistan. Sun kuma nanata cewa, ba wani aikin ta'addancin da zai dawo da kokarin Afghanistan baya na shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsarin demokiradiya a kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China