in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Turkiya za ta binciki sakaci game da tashin bam a gari dake kan iyaka
2013-05-15 10:01:06 cri

A ranar Talata, fraministan kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, kasar za ta binciko ko akwai sakaci game da tashin bama-bamai ranar Asabar a garin Reyhanli, wanda ke da iyaka da kasar Syria.

Erdogan ya bayyana wa 'yan majalisar dokokin kasar yayin jawabi a majalisar cewa, hukumar bincike ta ofishin fraministan kasar za ta gudanar da binicke game da tashin bama-bamai domin ta gano ko akwai sakaci kan lamarin, kuma waye ke dauke da alhakin hakan.

Ya cigaba da cewa, an fahimci wadanda ke da hannu a wannan lamari, da kuma wadanda aka yi amfani da su wajen kawo harin, inda ya kara da cewa, wata kungiyar kasar Turkiya dake da alaka da gwamnatin kasar Syria ita ce ta kai harin ta hanyar yin amfani da 'yan asalin kasar Turkiya.

Erdogan ya ce, ko shakka babu kasar Turkiya za ta rama wannan harin bama-bamai guda biyu da aka kawo mata kuma daidai wa daida, kana ya ci gaba da cewa, gwamnatin kasar ba za ta bari a shigar da Turkiya cikin yakin basasan da ake gwabzawa a kasar Syria ba.

Ya zuwa yanzu dai, kasar Turkiya ta tsare 'yan asalin kasar guda 13, saboda zargin cewa, suna da hannu a harin bama-baman wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 51, kana sama da 100 suka samu rauni a garin Reyhanli, inda dubban 'yan kasar Syria ke gudun hijira.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China