in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani hari ya hallaka mutum guda tare da jikkata 5 a Afghanistan
2013-05-22 15:11:45 cri

Rundunar 'yan sanda a birnin Ghazni, mai tazarar kilo mita 125 daga kudancin birnin Kabul na kasar Afghanistan, ta tabbatar da rasuwar mutum guda, baya ga wasu mutane 5 da suka jikkata sakamakon tashin wani abun fashewa da aka dasa a jikin wani keken hawa, da sanyin safiyar Larabar nan.

Mataimakin shugaban rundunar 'yan sandan lardin, Assadullah Khan ne ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarum kasar Sin Xinhua aukuwar wannan lamari, sai dai ya ce, kawo wannan lokaci, ba a tantance ko su waye aka yi nufin kaiwa harin ba.

Wannan dai hari ya zo ne daidai lokacin da 'ya'yan kungiyar Taliban ke dada kaimi wajen kai hare-hare kan dakarun gwamnati, da sojojin hadin gwiwa dake mara musu baya. Kawo dai wannan lokaci, akwai kimanin sojojin kungiyar NATO kimanin 100,000 jibge a kasar. Kuma tuni kungiyar ta Taliban ta umarci fararen hula, da su kauracewa tarukan hukuma, da jerin gwanon jami'an tsaro, tare kuma da yin kira gare su, da kada su nuna wani goyon baya ga gwamnatin kasar, da ma dakarun kasashen waje.

Yayin wani harin na daban da dakarun kungiyar ta Taliban suka kai, a wani shingen kan titi na jami'an tsaro a yankin Shar-e-Buzurg, dake Lardin arewacin Badakhshan, an ce, mahara 5 sun rasu, an kuma jiwa wani guda rauni. Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin gwamnatin lardin na Badakhshan, Abdul Maruf Rasikh ya ce, babu wani jami'in tsaro da ya samu ko da rauni yayin harin.

Hare-haren da kungiyar Taliban ke kaiwa dai a kasar ta Afghanistan, a bara kadai sun haddasa rasuwar dakarun gwamnatin kasar 2,800, da dakarun kasashen waje 400, baya ga fararen hula 2,754 da hare-haren suka hallaka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China