Wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kai hari kan wani ofishin 'yan sanda dake garin Rawa, mai tazarar kilomita 260 a arewa maso yammacin birnin Bagadaza, da yammacin ranar Lahadi 19 ga wata, harin da ya janyo dauki ba dadi tsakaninsu da 'yan sandan, ya kuma sabbaba rasuwar 'yan sanda 10 nan take.
Wata majiya da ta nemi a sakaye sunanta, ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, maharan sun tsere zuwa wani wurin da ba a tantance da shi ba, bayan aukuwar wannan lamari. Tuni dai aka tsaurara tsaro a garin na Rawa. Har ila yau a ranar ta Lahadi, wasu maharan sun bude wuta kan gungun wasu matasa a yankin Dora dake kudancin birnin Bagadaza, harin da ya janyo kisan mutum guda, tare da jikkata wasu mutanen su 5.
Kasar Iraki dai ta sha fama da yanayin tashe-tashen hankula a shekarun 2006 da 2007, lokacin da aka rika samun kashe-kashe tsakanin bangarori da ba sa ga maciji da juna, sai dai a iya cewa, yanzu yanayin tashe-tashen hankula na karuwa sannu a hankali, duk kuwa da sauki da aka dan samu a baya.(Saminu)