A ranar 4 ga wata da dare, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya yi shawarwari tare da sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka Hillary Clinton dake ziyara a birnin Beijing, ziyarar da ta zama ta biyu da Hillary ta kawo a nan kasar.
A yayin ganawa tasu, Yang Jiechi ya bayyana cewa, a wasu shekaru da suka gabata, an kiyaye ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata, kana an samu nasarori a wasu fannoni. Kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Amurka wajen kara inganta dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa daidaiton da shugaban kasar Sin Hu Jintao da shugaban kasar Amurka Barack Obama suka cimma, da kuma kafa sabuwar dangantaka a tsakaninsu.
Hillary ta bayyana cewa, ta yi farin ciki sosai da sake kawo ziyara a nan birnin Beijing da sake yin musayar ra'ayoyi tare da hukumomin kasar Sin. Kasar Amurka tana yin kokarin inganta dangantakar abokantaka a tsakaninta da kasar Sin, wannan muhimmin aiki ne ga kasar Amurka a kokarinta na samun daidaito a yankin Asiya da tekun Pasific. A cikin shekaru 3 da rabi da suka wuce, kasashen biyu sun gudanar da jerin shawarwari da ganawa a tsakanin shugabanninsu. A bana ne dai, kasashen biyu sun yi shawarwari bisa kan tattalin arziki da manyan tsare-tsare a zagaye na hudu, da kuma ganawa a karo na 12 a tsakanin shugabanninsu. (Zainab)