in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana son yin kokarin kawar da abin da zai yi illa ga ci gaban dangantakar dake tsakaninta da Amurka yadda ya kamata
2012-09-05 15:36:38 cri

A ranar 5 ga wata a nan birnin Bejing, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka Hillary Clinton, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana kara tuntubar juna da mu'amala da juna a tsakaninta da kasar Amurka, don kawar da abin da zai kawo illa ga ci gaban dangantakarsu yadda ya kamata.

Hu Jintao ya bayyana cewa, kiyaye dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka na da muhimmanci sosai ga farfadowar tattalin arzikinsu, har ma ga tattalin arzikin duniya baki daya. Yana fatan kasashen biyu za su yi amfani da fifikonsu domin inganta hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya. Hakazalika kamata ya yi a warware sabanin da ke tsakaninsu da ya shafi tattalin arziki da cinikayya, kana a magance maida matsalar tattalin arziki a siyasance. Ban da wannan kuma, yana son kasar Amurka za ta tsaya kan kin amincewa da kariyar cinikayya, kuma ta kawo sassauci kan kayyade fitar da kayayyakin fasaha zuwa kasar Sin, tare da samar da yanayi mai adalci ga kamfannonin Sin dake zuba jari a kasar Amurka.

Hillary ta ce, a shekaru 3 da suka wuce, kasashen biyu sun kiyaye tuntubar juna da hadin gwiwa da juna a tsakaninsu. Kasashen biyu sun inganta dangantakarsu yadda ya kamata. A halin yanzu, ana samun babban canji a duniya, kuma dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka na da muhimmiyar ma'ana. Kasar Amurka tana dukufa kan kawar da bambanci dake kasancewa a tsakaninta da kasar Sin, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu don tinkarar matsaloli da kalubalen da kasashen duniya ke fuskanta. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China