in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da sakatariyar harkokin waje ta Amurka Hillary Clinton
2012-09-05 20:54:15 cri
A yau Laraba ranar 5 ga wata, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya gana da sakatariyar harkokin waje ta Amurka Hillary Clinton a birnin Beijing.

A yayin ganawar, Wen ya bayyana cewa, dangantaka tsakanin Sin da Amurka na yin babban tasiri ga duniya baki daya. Tarihi ya nuna mana cewa, kasashen dake bin tsare-tsaren zaman al'ummar kasa iri na daban, suna iya yin zaman tare cikin lumana da samun bunkasuwa tare. Abu mafi muhimmanci shi ne shugabanni su yi la'akari da dangantaka tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni. Firaminista Wen ya ce, kamata ya yi Amurka ta girmamawa kasar Sin a fannonin ikon mulkin kasa da cikakken yankunan kasa, ta mai da hankali kan babbar moriyar kasar Sin da ra'ayin jama'ar kasar, tare da taka muhimmiyar rawa a cikin shawarwari da hadin gwiwar yankin Asiya da tekun Pasifik, a kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da neman samun bunkasuwa yadda ya kamata.

A nata bangare, Hillary Clinton ta amince da ra'ayin firaminista Wen, kuma ta ce, yanzu dangantaka tsakanin kasashen biyu na fuskantar sabon zarafi da kalubale. A sakamakon haka, neman samun moriyar juna da cimma nasara tare shi ya dace da moriyar kasashen biyu. Amurka na fatan kara mu'amala tsakanin manyan jami'ai da jama'ar kasashen biyu, da kara amfani da tsarin shawarwari iri daban daban, tare da kara samun fahimtar juna da hadin gwiwa tsakaninsu, ta yadda za su sa kaimi ga dangantaka tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.

A yammacin wannan rana har illa yau, mataimakin firaministan kasar Sin Li Keqiang shi ma ya gana da madam Clinton da 'yan rakiyarta a nan birnin Beijing.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China