A wannan rana, Li Keqiang ya gana da tsohon mai bada taimako ga shugaban kasar Amurka mai kula da harkokin tsaron kasa Stephen John Hadley, tsofaffin mataimakan sakatarorin harkokin wajen kasar Amurka biyu James B. Steinberg da Richard Lee Armitage, da kuma tsohon mai bada taimako ga ministan tsaron kasar Amurka Joseph S. Nye. Li Keqiang ya bayyana cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 40 da aka sake bude kofa ga juna a tsakanin Sin da Amurka. A cikin wadannan shekaru 40, an samu babban ci gaba kan dangantakar kasashen biyu domin kasashen biyu sun fahimci juna, yin hadin gwiwa da kuma warware manyan batutuwa tare. Ana bukatar kasashen biyu da su bi hanyar da ta dace, girmama juna, kara yin hadin gwiwa, daidaita matsalolin dake kasancewa a tsakaninsu da kuma yin mu'amala a tsakanin jama'arsu don inganta dangantakar abokantaka a tsakaninsu da neman hanyar bunkasa sabuwar dangantaka a tsakanin manyan kasashe.
Bangaren kasar Amurka ya amince da ra'ayin Li Keqiang game da raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kana ya bayyana cewa, ko jam'iyyar democrat ko jam'iyyar republican na kasar Amurka dukkansu su nuna goyon baya ga inganta dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin. (Zainab)