in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin ministocin tsaro na kasar Sin da Amurka
2012-09-18 11:42:40 cri
Yau Talata 18 ga wata da safe a nan birnin Beijing, ministan tsaron kasar Sin Liang Guanglie ya gana da takwaransa na kasar Amurka Leon Panetta.

Bayan ganawar, Liang Guanglie ya ce, shi da Leon Panetta sun cimma matsaya daya kan wasu manyan batutuwan dake jawo hankalinsu.

Liang Guanglie ya ce, Sin ta shirya sosai domin maraba da zuwan Leon Panetta zuwa nan kasar Sin. Mataimakin shugaban kasar Sin, kuma mataimakin shugaban kwamitin tsakiya na soja na kasar Xi Jinping, mataimakin shugaban kwamitin tsakiya na soja Xu Caihou, da mamban majalisar gudanarwa Dai Bingguo sun gana da Leon Panetta. Ban da wannan kuma, Leon Panetta zai kai ziyara kwalejin sojoji injiniyoyi na motocin sulke, inda zai yi jawabi da cin abinci tare da dalibai.

Leon Panetta ya ce, kasashen biyu sun kasance manyan kasashe a yankin Asiya da Pacific, bangarorin biyu dukkansu suna dora muhimmanci kan abubuwan da suka shafi yaki da ta'addanci, hana yaduwar makaman nukiliya, samar da taimakon jin kai, yaki da sumogar miyagun kwayoyi, kiyaye ikonsu a kan teku, kiyaye zaman lafiya da sauransu. Kafa wata dangantaka mai inganci tsakanin sojojinsu ya zama abu mai muhimmancin gaske don sa kaimi ga ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashen 2. Ban da wannan kuma, ya kamata shugabannin kasashen biyu su kara kai wa juna ziyara, da kara fahimtar juna da kuma kawar da bambancin ra'ayi tsakaninsu.

Ziyarar Leon Panetta a kasar Sin ta kasance karo na farko tun bayan da ya zama ministan tsaron kasar Amurka a shekarar 2011.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China