in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kasar Sin ya gana da ministan tsaron kasar Amurka
2012-09-19 20:58:01 cri

A safiyar yau Laraba 19 ga wata, mataimakin shugaban kasar Sin, kana mataimakin shugaban kwamitin soja na tsakiya na kasar, Xi Jinpin ya gana da ministan tsaron kasar Amurka, Leon Panetta da 'yan rakiyarsa a nan birnin Beijing.

A lokacin ganawar, Xi ya bayyana matsayin da kasar Sin take kan batun tsibirin Diaoyu, inda ya ce, wasu jam'iyyun kasar Japan ba ma kawai ba su son zaman lafiya da kasashe makwabtanta da ma sauran kasashen Asiya da na tekun Pasifik a sakamakon yake-yaken da kasar ta yi ba, haka kuma ya kasance har ma su naci gaba da yin kuskure game da yunkurin sayen tsibirin Diaoyu, tare da tababa cewa sanarwar Cairo da ta Potsdam ba su da karfin dokokin kasa da kasa, a yunkurin tsananta batun mallakar yanki tsakanin kasar Japan da makwabtanta da sauransu.

Mataimakin shugaban kasar na Sin ya ce, kamata ya yi Japan ta dakatar da keta mulkin kai da ikon mallakar cikakken yankin kasar Sin nan take. Kuma yana mai fatan kasar Amurka za ta yi taka-tsamtsam, ta guji saka hannu cikin batun tsibirin Diaoyu, ko gudanar da ko wane irin ayyukan da za su tsananta yanayin da ake ciki a yanzu.

A nasa bangaren kuma, Leon Panetta ya furta cewa, makasudin manufar sake samun daidaito a Asiya da tekun Pasifik da Amurka ke dauka shi ne sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun wadata a wannan shiyya. A kokarin cimma wannan buri, in ji shi, abin da ya fi muhimmanci shi ne kulla hulda mai mana'a tsakanin Amurka da Sin. A sabili da haka, Amurka na fatan kara yin shawarwari da kasar Sin, da karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu, a kokarin kafa sabuwar dangantaka a tsakanin wadannan manyan kasashen biyu.

Dadin dadawa, Panetta ya ce, Amurka ba za ta sa hannu kan matsalar mallakar yankin kasa ba. Don haka ma ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su daidaita wannan batu cikin lumana, a maimakon nuna cigaba da takalar ga juna.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China