in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka
2012-09-05 11:15:48 cri

A ranar 5 ga wata da safe a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka Hillary Clinton, kuma wannan ne karo na biyu da Hillary ta kawo ziyara nan kasar Sin cikin wannan shekara.

Hu Jintao ya yi maraba da zuwan Hillary, ya ce wannan ne karo na bakwai da Hillary ta kawo ziyara nan kasar Sin tun bayan hawan mukaminta, kuma daga cikinsu sau hudu ta zo ne domin shugabantar shawarwari kan tattalin arziki da manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Amurka, a yayin da sau uku ta zo ne domin halartar shawarwarin al'adu a tsakanin bangarorin biyu.

Hillary daga nata bangare ta ce, ta yi farin ciki sosai da sake kawo ziyara nan birnin Beijing da kuma ganawa da shugaba Hu Jintao. A shekaru 3 da suka wuce, kasashen Amurka da Sin sun yi hadin gwiwa da shawarwari sau da yawa. Shugaba Hu Jintao da shugaban kasar Amurka Barack Obama sun yi ganawa karo na 12 a gun taron koli na G20 da aka gudanar a kasar Mexico, kuma kasar Amurka ta nuna yabo ga nasarorin da aka samu a shawarwari kan tattalin arziki da manyan tsare-tsare.

Kana Hillary ta bayyana cewa, idan an yi hangen nesa, mu'amala a tsakanin jama'ar kasashen biyu ya zama tushe wajen inganta dangantakar kasashen biyu. A karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, Amurka ta yi kokari kuma ta kara tuntubar juna da hadin gwiwa da juna a fannoni daban daban tare da kasar Sin. A ganinta, hanyar inganta dangantaka a tsakanin kasashen biyu tana bisa tushe mai karfi a yanzu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China