A ranar Litinin ne aka kammala taron kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU kashi na 21 wanda ya fado daidai da bukin cika shekaru 50 da kafa kungiyar, inda shugabanni suka kudurta kara himma wajen hadin kai da zaman lafiya a nahiyar.
Da yake jawabi a gun bukin kammala taron, framinsitan kasar Habasha kuma shugaban karba karba na kungiyar AU a wannan karo, Hailemariam Desalegn, ya ce, wannan kuduri yana da muhimmanci domin ya nuna anniyar kawo gagarumin sauyi a nahiyar a wannan karni na 21.
Ya ci gaba da cewa, shugabannin nahiyar sun kuma kara himma daukar matakan da suka dace na cimma burin kudurorin da aka zana a yayin taron.
Ya ce, 'Yayin da muke nazarin nasarori da aka cimma a baya da ma kalubale, mun sake jan damarar kara sadaukar da kai bisa manufofn hadin kan Afirka duk da girma da take da shi.'
A gun taron tattaunawa game da dunkulewar kasashen Afrika da farfado da nahiyar, shugabar kwamitin kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma, ta yi kira da a gaggauta yunkurin dunkulewar kasashen Afrika baki daya, ta hanyar tilasta aikin kafa yankunan yin cinikayya cikin 'yanci a kasashen Afrika.
Haka kuma, a yayin taron, an tsaida kudurin kafa wata rundunar ko-ta-kwana, don magance kalubalen dake shafar harkokin tsaro a nahiyar, matakin da ake fatan zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da karko a kasashen Afrika.
Da yake kuma an shirya taron na wannan karo ne dangane da cika shekaru 50 da kafa kungiyar hadin kan kasashen Afirka, bukin da aka shirya a hedkwatar dake kasar Habasha, inda a can ne aka fara kafa kungiyar a shekarar 1963, ya samu zuwan shugabanni daga wajen nahiyar.(Lami)