in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika na hangen gaba, in ji AU
2013-05-23 12:28:56 cri

A jajibirin bikin cikon shekaru 50 da kafuwar tarayyar Afrika AU a ranar 25 ga watan Mayu, nahiyar Afrika na hangen gaba tare da sanya kokari matuka domin neman samun makoma mai kyau a cikin 'yan shekaru masu zuwa, in ji shugabar kwamitin tarayyar Afrika AU, madam Nkosazana Dlamini-Zuma a ranar Laraba a birnin Geneve. Yanzu lokaci ne da ba na wasa ba a duniya baki daya, domin kwanaki 1000 suka rage kafin mu shiga shekarar 2015, da kuma tsara shirye-shiryen bayan shekarar 2015 a nahiyar Afrika, in ji madam Dlamini-Zuma a yayin wani dandalin kasa da kasa kan kiwon lafiya karo na 66. Daya daga, abu mafi muhimmanci cikin manyan batutuwan da Afrika ta sanya gabanta shi ne mai da hankali da kuma zuba jari kan al'ummarta da yawansu zai kai biliyan biyu nan da shekarar 2050, kuma kashi 50 cikin 100 daga cikinsu zai kasance na matasa 'yan kasa da ba su kai shekaru 18 da haihuwa, tare da samar da ayyukan jinya ga kowa domin duk wani cigaban kasa ba zai samu ba idan ba'a tabbatar da ilimi da kiwon lafiya ga jama'a ba, a cewar Nkosazana Dlamini-Zuma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China