A jiya alhamis 23 ga wata kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta yi alawadai da harin kunar bakin wake da aka kai a garuruwan Arlit da Agadez na jamhuriyar Nijar.
Cikin wata sanarwa, shugabar kungiyar Nkosazana Dlamini-Zuma ta yi suka da babbar murya kan wadannan hare-hare har guda biyu da suka auku a safiyar jiyan, tana mai nuna cikakken goyon bayanta ga gwamnatin kasar Nijar a kokarinta na yaki da ta'addanci.
Haka kuma madam Zuma ta jaddada godiyarta ga kasar ta Nijar bisa ga gudunmuwar sojin da ta bayar domin taimaka ma wata kasar a nahiyar wato Mali yakan ta'addanci.
Shugabar kungiyar ta AU ta ce, tsagerancin 'yan ta'adda a Nijar ya nuna bukatar dake akwai ga daukacin kasashen Afrika da su hada kai su yake wannan batu tare da sauran miyagun ayyuka da suka ratsa cikin nahiyar.(Fatimah)