in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira da a kai zuciya nesa a Guinea
2013-05-13 10:01:48 cri

Kungiyar hadin kan Afirka ta AU ta yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su kai zuciya nesa, tare da rungumar sulhu, a matsayin hanya daya tilo, ta magance barkewar rikici a kasar Guinea Conakry.

Wannan kira ya zo daidai lokacin da aka shiga halin dar dar, tare da aukuwar 'yan tashe-tashen hankula yayin zanga-zanga mai alaka da siyasa da ta wakana a kasar.

Wata sanarwa da shugabar kungiyar ta AU Nkosazana Dlamini- Zuma ta fitar a karshen makon da ya gabata, ta bayyana matukar bukatar da ake da ita, ta dukkanin bangarori masu ruwa da tsaki, ciki hadda tsagin gwamnati da na 'yan adawa, da su martaba yarjejeniyar kaucewa ta da husuma da aka amince da ita a ranar 23 ga watan Afirilun da ya gabata.

Har ila yau, Zuma ta jaddada muhimmancin wanzar da zaman lafiya da tsaro a dukkanin fadin kasar, matakin da ba za a kai ga samunsa ba, har sai dukkanin masu ruwa da tsaki sun ba da tasu gudummawa.

Ta ce, daukar wannan mataki na rungumar sulhu, zai ba da damar gudanar da managarcin zaben 'yan majalissun dokokin kasar dake tafe, matakin da kuma, a cewarta, zai yi matukar karfafa salon mulkin dimokaradiyyar kasar.

Daga nan sai uwar gida Zuma ta bayyana cikakken goyon bayan AU, ga tawagar masu ba da taimako na MDD, karkashin jagorancin wakilin musamman na magatakardar majalissar mai lura da yammacin Afirka Said Djinnit, wanda bisa tallafinsa, aka samu ci gaba mai yawa ta fuskar samar da daidaito a kasar ta Guinea. Har ila yau, AU ta jaddada goyon bayanta, ga dukkanin wani shiri da zai taimaka a kai ga cimma nasarar wanzar da zaman lafiya da karko, da gudanar da zabe mai inganci a kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China