A jawabinsa wajen wannan gaggarumin biki Haile Mariam ya bayyana samar da kayyakin more rayuwa a matsayin wani babban abin da za'a maida hankali a kai a shekaru masu zuwa don ganin yadda za'a gaggauta cigaba a kuma samar da wassu hanyoyin karuwar tattalin arziki a nahiyar.
Haile Mariam ya kuma lura cewa samar da kayayyakin more rayuwa wani bangare ne da aka yi watsi da shi a shekarun baya kuma rashin isassun kayayyakin na daya daga cikin abubuwan da suka durkushe cigaba kuma wanda ke ci ma nahiyar tuwo a kwarya gami da kawo cikas ga samun sauyi a fannin tattalin arziki.
Shugaban na AU ya lura da cewa abin alfahari ne yadda wassu abokan arziki na nahiyar da kuma abokan hadin gwiwa suka dora babban muhimmanci wajen ganin sun taimaka da ababen more rayuwa a nahiyar ta hanyar samar da dabaru a fannin hadin gwiwa wanda in ji shi,ya sa ya zama wajibi ya nuna matukar godiyarsa ga kasar Sin wadda ta zuba jari na dumbin kudade a wannan fanni domin taimaka ma nahiyar ta samu cigaba.(Fatimah Jibril)