in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AU ta yi bikin cika shekaru 50 da kafuwarta
2013-05-26 16:47:51 cri

Kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU, wadda asalin sunata a da kungiyar hada kan kasashen Afirka OAU, ta yi bikin tunawa da kafuwarta shekaru 50 da suka wuce, a birnin Adis Ababa na kasar Habasha, a ranar Asabar 25 ga wata, inda aka waiwayi tarihin kungiyar da nasarorin da ta cimma, gami da tattaunawa kan yadda za a tabbatar da zaman lafiya da samun walwala a nahiyar Afirka. A wannan rana, kungiyar AU ta kira taron tattaunawa mai taken 'ra'ayin Pan Afirka da farfadowar nahiyar', inda shugaban karba-karba ta kungiyar, kuma firaministan kasar Habasha, Haile Mariam Desalegne, a cikin jawabin sa yace, a shekaru 50 da suka wuce, kuma bisa jagorancin ra'ayin Pan Afirka, kasashen Afirka sun samu 'yancin kai da ci gaban tattalin arzikinsu. Nan gaba, nahiyar Afirka za ta dukufa kan rage talauci, da kwantar da kurar dake tashi, sa'an nan a sanya yawancin kasashen nahiyar su cimma matsakaicin matsayi a fannin kudin shiga. Don haka, yana ganin cewa, ya kamata kasashen Afirka su kara ware kudi don raya aikin noma, da samar da kayayyakin more rayuwa, gami da tallafawa kamfanoni masu zaman kansu.

A nasa bangaren, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin firaministan kasar Sin, Wang Yang, wanda ya halarci taron kungiyar AU musamman domin taya murnar zagayowar ranar cika shekaru 50 da kafa kungiyar OAU, ya karanta sakon taya fatann alheri daga shugaba Xi Jinping na kasar Sin. A cikin sakon sa, shugaba Xi ya yaba ma kokarin kungiyar OAU a fannin neman 'yancin kan nahiyar Afirka, da kawar da kabilanci, da gudummawar da ta samar. Sa'an nan ya nuna niyyar gwamnatin kasar Sin na son rufa ma kasashen Afirka baya a kokarinsu na ganin dinkuwar junansu waje daya don neman samun ci gaba, kana kasar Sin na son yin kokari tare da kasashen Afirka don zurfafa huldar dake tsakanin bangarorin 2, wadda ta shafi manyan tsare-tsare. A lokacin taron, Wang Yang ya gana da shugaban karba karba na kungiyar AU Haile Mariam Desalegne, da shugabar kwamitin kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma, inda suka yi musayar ra'ayi kan dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, tare da cimma matsaya daya a batutuwa da dama, inda a cewar Wang Yang, idan kungiyar AU ta samu ci gaba, nahiyar Afirka ita ma za ta samu damar bunkasa kanta. A zamanin yanzu, ana fuskantar sabuwar damar kulla huldar hadin kai tsakanin bangarorin Sin da Afirka, don haka Sin na son yin kokari tare da kungiyar AU, don kyautata tsarin da ake bi a kokarin hadin kai, da kara yin mu'amala yayin da suke daidaita al'amuran duniya, ta yadda za a samu damar kyautata huldar dake tsakanin bangarorin 2 zuwa wani matsayi mai nagarta. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China