A ranar Lahadi 26 ga watan nan ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, wanda yake ziyara a kasar Jamus ya gana da takwaransa Madam Angela Dorothea Merkel a fadar firaministan kasar ta Jamus.
Yayin ganawar tasu, jagororin biyu sun tsaida shirin hadin gwiwa tsakanin kasashen nasu a nan gaba, tare kuma da cimma matsaya kan bunkasuwar dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare.
Li Keqiang ya ce, Sin da Jamus jigajigan kasashe ne na duniya, hadin gwiwa da suke yi tsakaninsu ba ma kawai ya dace da moriyarsu na kansu ba, har ma ya taimaka ga dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Turai, dama dukkanin kasashen duniya.
Li Keqiang ya kara da cewa, kasar Sin kullum take daukar Turai bisa matsayin manyan tsare-tsare, tana nacewa ga nuna goyon baya ga yunkurin dunkulewar nahiyar Turai, haka ma ga kokarin da kungiyar EU ke yi na warware matsalar basusukan dake addabar nahiyar, da tabbatar da tattalin arzikin nahiyar Turai mai karko.
A nata bangare Angela Dorothea Merkel ta ce, Jamus na goyon bayan kara hadin gwiwa tsakanin Turai da kasar Sin, ta kuma tsaya kan matsayin warware matsalolin da suka wakana a wannan fanni ta hanyar yin shawarwari, da kara habaka ciniki tsakaninsu, ta yadda za su ci moriyar juna da kawar da bambancin ra'ayi.
Bayan ganawar tasu, firaministocin biyu sun gane ma idanunsu yadda aka sa hannu kan wasu yarjeniyoyi a fannonin zubawa juna jari, da yin tsimin makamashi, da kiyaye muhalli, da sha'anin noma, da ba da ilmi da dai sauransu. (Amina)