A yayin wata liyafa da aka shiryawa wasu masana tattalin arziki da hada-hadar kudi, Li yana mai cewa, tattalin arzikin kasar Sin na samun daidaituwar bunkasuwa tun farkon wannan shekara, saurin karuwar tattalin arzikin a farkon watanni uku na bana ya kai kashi 7.7 bisa dari, ko da yake ya ragu kadan bisa na makamancin lokaci na bara, amma ya fi da yadda aka yi tsamani na kashi 7.5 bisa dari. A sa'i daya kuma, yawan mutanen da suka samun aikin yi ya karu, a cikin farkon watanni hudu na bana, yawan mutane da suka samu aikin yi a garuruwa ya kai miliyan 4.7, sannan ba a samu hauhawar farashin kayayyaki sosai ba wadda ta kai kashi 2.4 bisa dari. (Amina)