Firaministan da yake ziyarar aiki a kasar Jamus ya fadi hakan ne lokacin da ya ziyarci Fadar Cecilienhof dake garin Potsdam babban birnin jihar Brandenburg, inda a nan ne aka rattaba hannu a kan Yarjejeniyar Potsdam a shekara ta 1945, wadda ta jaddada amincewar da aka yi a Alkahira wadda ya tabbatar da cewa kasar Japan dole ne ta mayar da dukkannin yankuna na kasar Sin da ta karbe.
Mr. Li yace, Tarihi wani abu ne da yake tattara bayanai na gaskiya kuma lallai sai an yi amfani da su yadda ya kamata ne za'a iya hango abin da ke zuwa a gaba. Haka kuma a cewar shi, duk wani yunkuri da zai sa a ki amfani da hakan ko kuma a yi ma wadanda suka yi yaki domin danniya kirari a wannan lokaci ba wani abu ba ne illa wani kalubale da ake son kawo ma yin adalci ga kasashen duniya, abin da kuma Sinawa ba za su taba amincewa da shi ba, kuma za'a yi tir da shi a duniya baki daya.(Fatimah Jibril)