in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya isa kasar Switzerland
2013-05-24 15:26:10 cri

Bisa gayyatar da shugaban kasar Switzerland Ueli Maurer ya yi masa, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya tashi daga kasar Pakistan a daren jiya Alhamis 23 ga wata, kuma ya isa birnin Zurich na kasar Switzerland, domin fara ziyarar aiki.

Mataimakin shugaban kasar, kuwa ministan harkokin waje Didier Burkhalter ne ya tarbi Li Keqiang a filin saukar jiragen sama. Inda Li Keqiang ya gabatar da jawabi a rubuce, cikin jawabin nasa ya ce Switzerland ta kasance daya daga cikin wasu kasashen yamma, da suka kafa dangantakar diplomasiyya da kasar Sin tun da farko, kuma ita ce muhimmiyar kawar hadin gwiwa ta kasar Sin a nahiyar Turai a fannonin tattalin arziki, da kimiyya, da kuma hada-hadar kudi.

Li Keqiang ya ziyarci Switzerland ne a farkon wannan zango na aikinsa, a matsayin firaministan kasar Sin, da zummar kara karfafa mu'amala tsakanin shugabannin kasashen biyu, ta yadda za a ingiza hadin gwiwa, da habaka moriyar juna, da ma batun zurfafa zumunci dake tsakanin jama'ar kasashen biyu, da kuma raya dangantakar sada zumunci tsakaninsu yadda ya kamata cikin dogon lokaci.

Yayin wannan ziyara, Li Keqiang zai gana da shugaban kasar Ueli Maurer, zai kuma gabatar da jawabi ga masanan tattalin arziki da na kudi, tare da yin mu'amala da jama'ar kasar. Ban da haka kuma, ana sa ran kasashen biyu, za su kulla wasu yarjeniyoyin hadin kai a fannoni tattalin arziki, da cinikayya, da hada-hadar kudi, da kwadago, da kuma ilimi da dai sauransu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China