Li ya bayyana cewa, bayan da aka sanar da bude shawarwarin yin ciniki cikin 'yanci a shekaru 3 da suka gabata, bangarorin biyu sun yi kokari da kuma cimma wata yarjejeniyar yin ciniki cikin 'yanci mai samun moriyar juna, wannan ne yarjejeniya ta farko da Sin da wata kasar Turai suka kulla a wannan fanni, wadda kuma take da babbar ma'ana ga zurfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Switzerland har ma da sauran kasashen Turai.
Mr Maurer ya ce, Sin muhimmiyar abokiyar kasarsa Switzerland ce. An samu nasarori da dama ta hanyar ziyarar Li Keqiang, kana kasashen biyu sun cimma yarjejeniyar yin ciniki cikin 'yanci da bude shawarwarin hada-hadar kudi. Don haka Kasarsa za ta sa ido sosai kan wannan dama, kuma tana son kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu da kuma samun bunkasuwa tare. (Zainab)