A jiya Asabar 25 ga wata, Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa kasar Jamus, wadda ita ce kadai kasa daga nahiyar Turai da ya ziyarta a cikin ziyarar aikin da ya kai kasashen waje a karo na farko tun darewarsa wannan mukamin.
A wata sanarwa da aka fitar jim kadan da saukarsa, Li Keqiang yace ganin Jamus ce kadai kasa a nahiyar Turai da ya ziyarta a ziyarar shi na farko kasashen waje, hakan na nuna irin muhimmancin da Sin ta dora na ganin ta inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da ma nahiyar Turai.
Mr. Li yace, Sin da Jamus kasashe ne masu muhimmanci a duniya, inganta abotan hadin gwiwwa da kasar wani zabi ne da Sin ta yi bisa manyan tsare-tsare cikin dogon lokaci.
Ya yi bayanin cewa, Sin a shirye take ta yi aiki da kasar Jamus kafada da kafada domin inganta amincin dake tsakaninsu, kara fahimtar juna, fadada hadin kai da kuma karfafa cudanyarsu a bangarori daban daban na duniya da ma na shiyya-shiyya, a kokarin ciyar da dabarun hadin gwiwwa gaba tsakaninsu har ma da sauran kasashen Turai tare.
A lokacin wannan ziyarar, Firaminista Li zai gana da Shugaban kasar Jamus Joachim Gauck, sannan zai tattauna da Shugabar Gwamnatin kasar Uwargida Angela Merkel. Zai kuma gabatar da jawabi a wani taro na 'yan kasuwa, sannan yayi musayar ra'ayi da manyan 'yan siyasa da 'yan kasuwar kasar ta Jamus.
Haka kuma Mr. Li tare da Shugabar Gwamnatin Angela Merkel za su kaddamar da shirin shekarar harsuna, wanda shiri ne tsakanin kasashen biyu da zai taimaka ma aniyarsu ta koyon harsunan juna.
Domin kara inganta hadin kai a tsakanin kasashen biyu, za a daddale wasu yarjeniyoyi a fannoni kamar na samar da tsimin makamashi, kare yanayi, zuba jari , aikin gona da samar da ilimi.(Fatimah Jibril)