in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da shugaban Jam'iyyar Pakistan Muslim League
2013-05-23 20:55:19 cri

Firaminitan kasar Sin Li Keqiang ya gana da Muhammad Nawaz Sharif, shugaban Jam'iyyar Pakistan Muslin Leage a ranar 23 ga wata a Islamabad, babban birnin kasar Pakistan.

A yayin ganawar, Li ya taya Sharif murnar samun nasara a babban zaben majalisar dokokin kasar da aka gudanar ba da dadewa ba. Kuma ya bayyana cewa, sabuwar gwamnatin kasar Sin za ta yi kokari tare da Pakistan don ci gaba da sada zumunta a tsakaninsu, da inganta hadin gwiwar da ke tsakaninsu, domin bude wani sabon shafi ga ci gaban dangantaka a tsakanin kasashen biyu.

Haka kuma Li ya nuna cewa, kasar Sin na son tattaunawa tare da kasar Pakistan kan yadda za su inganta hadin kai ta fuskar tattalin arziki da cinikayya daga dukkan fannoni, musamman ma a fannin tsara wani shiri don fito da wata kafar da za su bunkasa tattalin arzikinsu, ta yadda zai zama wani sabon sakamako mai kyau wajen hadin kansu.

A nasa bangaren,shugaba Sharif ya yi maraba da zuwan Li Keqiang a Pakistan, ya kuma kara da cewa, kasar Sin babbar aminiya ce ta Pakistan. Nuna aminci ga kasar Sin buri ne na dukkan al'ummar Pakistan, kuma aiki ne mafi muhimmanci ga ko wace jam'iyyar da ke kan karagar mulkin kasar. Pakistan na da aniyar inganta hadin kai tare da kasar Sin, da kuma aiwatar da sakamako masu kyau da aka samu yayin wannan ziyara bisa iyakacin kokarinta. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China