A jiya laraba 22 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang wanda ya isa Islamabad babban birnin kasar Pakistan domin ziyarar aiki ya sadu da Shugaba Asif Ali Zardari.
Da farko, Li Keqiang ya isar da gaisuwa da kyakkyawar fatan shugaba Xi Jinping inda daga bisani ya nuna cewa, Sin da Pakistan abokai ne a dukkan fannoni, kuma dangantakar dake tsakaninsu na da tushe mai inganci sannan tana da makoma mai haske musamman ganin yadda tun lokacin da Shugaba Asif Ali Zardari ya kama aikinsa ya ziyarci kasar Sin har sau 9, abin da ya taka muhimmiyar rawa ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma kasar Sin ta yaba da hakan sosai.
Li Keqiang ya ce, wannan shi ne karo na farko da ya ziyarci kasar Pakistan tun hayewar sa wannan mukamin don haka yana da zummar inganta hadin gwiwa da Pakistan ta yadda kasashen biyu za su raya dangantakar dake tsakaninsu bisa sabon mataki tare kuma da bunkasa dangantakar zuwa wani sabon matsayi.
A nashi bangaren Shugaba Asif Ali Zardari kuwa ya nemi Li Keqiang ne da ya isar da gaisuwarsa zuwa ga Shugaba Xi Jinping, yana mai cewa, ziyarar firaministan a Pakistan ya shaida cewa, gwamnati da jama'ar kasar Sin sun mai da muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, don haka sada zumunci da kasar Sin ya kasance matsaya daya da gwamnati da al'ummar Pakistan suka cimma gaba daya. Shugaba Ali Zardani ya ce Pakistan na fata hadin gwiwa da kasar Sin domin ingiza dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin su. (Amina)