Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar samun bunkasuwa cikin lumana, kana ta tabbatar da ikon mulkin kasar da cikakken yankunanta, wadanda suka dace da halin kiyaye zaman lafiya a yankin da kuma ka'idojin tabbatar da zaman lafiya na duniya. A halin yanzu, kasar Sin tana fuskantar yanayin bunkasuwar tattalin arziki na duniya mai sarkakkiya, kana ana fuskantar tafiyar hawainiya wajen samun farfadowar tattalin arzikin duniya, da samun ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, kana wasu kasashe sun dauki manufofin kudi masu sassauci wadanda za su kawo illa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Game da wannan, kasar Sin tana kokarin tinkarar su, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da sauran kasashen duniya. Kasar Sin za ta ci gaba da bin manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a cikin gida, da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin kasar ta hanyar raya masana'antu, sadarwa, birane da kauyuka, don kara samar da kyakkyawar dama ga tattalin arzikin duniya.
Ban da wannan kuma, Li Keqiang yana begen yin shawarwari tare da shugabanni da jama'a daga bangarori daban daban na kasar Pakistan kan yadda za a zurfafa hadin gwiwar kasashen biyu a dukkan fannoni, ta yadda za a kyautata rayuwar jama'ar kasashen biyu a nan gaba. (Zainab)