in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya fara ziyara a kasar Pakistan
2013-05-22 20:04:21 cri
Bisa gayyatar da gwamnatin Jamhuriyar Pakistan ta yi masa ne, Mr. Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya isa birnin Islambad yau 22 ga wata da safe bisa agogon wurin, inda ya fara ziyarar aiki a kasar Pakistan.

Bayan saukarsa a filin saukar jiragen sama na Islambad, Li Keqiang ya bayar da wani jawabi a rubuce, inda ya ce, bunkasa huldar sada zumunci tsakanin kasar Sin da kasar Pakistan manufa ce da gwamnatin kasar Sin ke dauka a kullum. Ko da yake ana samun sauye-sauye sosai a duniya da kuma a yankin, duk da haka, gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan matsayinta na karfafa da kuma bunkasa huldar sada zumunci tsakaninta da kasar Pakistan, kuma tana goyon bayan kasar Pakistan wajen tabbatar da 'yancin mulkin kasa, cikakken yankunanta, kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasar.

Li Keqiang ya kara da cewa, yana fatan ziyararsa za ta ba da gudummawa wajen sada zumunci da karfafa hadin gwiwa da kuma tsara babban shirin neman bunkasuwa a tsakanin kasashen biyu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China