Shugaban al'ummar Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya ce, ba za a amincewa Yahudawa 'yan kama wuri zauna, su ci gaba da shiga wani wurin Ibada da ake wa lakabi da bangon yamma, da ke birnin Kudus ba. Kamfanin dillancin labarai na WAFA, ya rawaito Abbas, na wannan tsokaci ne ranar Lahadi 12 ga wata, yayin da ya halarci taron kungiyar PLO a birnin Ramalla, dake yamma da gabar kogin Jordan.
A farkon wannan wata na Mayu ne dai, kasar Isra'ila, ta amincewa Yahudawa shiga wannan wuri na bauta, domin tunawa da kewayowar lokacin da birnin Kudus ya sake hadewa, duk kuwa da rashin amincewar da Falasdinawa suka nuna ga hakan. Wannan batu na bijirowa ne dai, a gabar da Amurka ke kokarin shiga tsakanin bangarorin biyu, domin farfado da batun shawarwari tsakanin Isra'ilan da al'ummar Falasdinawa.
An dakatar da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu ne, tun cikin shekarar 2010, sakamakon rashin jituwa kan batun ginin matsugunnan Yahudawa a yamma da gabar kogin Jordan, da kuma gabashin birnin Kudus.
A baya-bayan nan ma dai, sai da jakada na musamman, kuma jagoran masu shiga tsakani a yankin gabas ta tsakiya Tony Blair, ya yi kira ga Isra'ila, da ta martaba hakkin masu ibada, ta kuma kare mutunci, da alfarmar wuraren Ibada. Ya ce, ya damu matuka da halin da ake ciki a birnin Kudus, musamman duba da yadda aka fuskanci yanayin tashin hankali, a lokaci bukukuwan Ester da ya gabata.(Saminu)