Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya yi bayani yau Juma'a cewar, nasarar da Palesdinu ta cimma wato a ba ta matsayin kasa 'yar kallo a MDD ta dace, domin za ta zamo matakin farko na cimma burinta na zaman kasa mai 'yanci.
Cikin wata sanarwar da aka bayar a safiyar Juma'a, wasu 'yan sa'o'i bayan babban taron MDD ya yi gagarumin kuri'ar nuna cikakken goyon baya ga daukaka matsayin Palesdinu a MDD, wato daga matsayin yanki zuwa kasa wace ba mamba ba, Hong Lei na mai cewa, wannan mataki ya nuna cewar, bukatar mutanen Palesdinu na ganin an maido masu 'yancinsu na kasa ya samu gagarumin goyon baya daga al'ummar duniya.
Ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta jefa kuri'ar nuna goyon baya tare da sauran kasashe mambobin MDD.
Hong Lei ya ce, kasar Sin a ko da yaushe tana mai ra'ayin cewa, kafa Palesdinu a matsayin kasa mai cikakken iko, 'yanci ne na 'yan Palesdinu, kuma shi ne zai zamo wani tushe, kana abin bukatar da zai kai ga cimma zaman lumana tsakanin Palesdinu da Isra'ila.
Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da daukar kyawawa da kuma muhimman matakai na ganin an cimma warware batun Palesdinu cikin adalci.(Lami)