Wannan jami'i ya bayyana cewa, bayan da aka aiwatar da manufar bude kofa da yin kwaskwarima a kasar Sin, an samu babbar nasara kan ciniki tsakanin Sin da kasashen waje. Kuma kasar Sin ta kasance wata babbar kasa ta ciniki. Amma matsalolin rashin daidaito da kasa samun bunkasuwa mai dorewa suna ci gaba da kasancewa, sabo da haka, ya kamata kasar Sin ta gaggauta canja hanyar samun bunkasuwar ciniki. Don tabbatar da gudanar da aikin canja hanyar, tilas ne a sa kaimi ga kyautata tsarin ciniki tsakanin Sin da kasashen waje ta hanyoyin inganta kayayyakin da kasar take fitar zuwa kasashen waje, daga karfin kamfanonin Sin, sa kaimi ga gwamnatin kasar da ta shiga aikin tsara ka'idojin cinikin duniya, kyautata kasuwar duniya a fannin ciniki, da kuma kafa tsarin nuna goyon baya ga ciniki daga dukkan fannoni, ta haka kasar Sin za ta canja matsayinta daga babbar kasa zuwa kasa mai karfi a fannin ciniki a duniya.(Zainab)