Ranar 16 ga wata, a gun taron manema labaru da aka saba yi a ko wane wata, kakakin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Shen Danyang ya nuna cewa, Sin za ta fuskanci kalubale mai tsanani wajen tabbatar da samun bunkasuwar cinikayyar waje na kashi 10 bisa dari a wannan shekara, saboda illar da rikicin basusukan nahiyar Turai ya haifar da kuma kasa samun karfin farfado da tattalin arzikin duniya.
Bisa kididdigar da aka bayar an ce, a cikin watan Yuli, yawan kudin da Sin ta samu wajen fitar da kayayyaki ya kai dala biliyan 176.94 wanda ya karu da kashi 1 bisa dari, yayin da kudin da ta kashe wajen shigo da kayayyaki ya kai dala biliyan 151.79 wanda ya karu da kashi 4.7 bisa dari. Shen Danyang ya ce, dalilin da ya sa saurin karuwar kayayykin fitarwa ya ragu cikin sauri shi ne yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashen Turai ya ragu sosai a watan Yuli. A wannan wata, yawan kudin da Sin ta samu ta fuskar fitar da kayayyaki zuwa tarayyar Turai ya kai dala biliyan 29.37 wanda ya ragu da kashi 16.6 bisa dari.
Ban da wannan kuma, kididdigar da ma'aikatar cinikayyar ta bayar ta nuna cewa, daga watan Jarairu zuwa Yuli, 'yan kasuwa na kasar Sin sun zuba jari ga kamfanoni 2407 na kasashe ko yankuna 117 a duniya, yawan kudin ya kai dala biliyan 42.22, wanda ya karu da kashi 52.8 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. (Amina)