in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An maido da kiwon lafiya a lardin Sichuan da girgirzar kasa mai tsanani ya shafa
2013-05-03 15:16:36 cri

Hukumar kiwon lafiya da kayyade iyali ta kasar Sin ta ba da wata sanarwa a ran 2 ga wata cewa, ana gudanar da aikin ba da jiyya da yin ringakafi yaduwar cutattuka yadda ya kamata a lardin Sichuan baki daya, inda girgizar kasa mai tsanani ta auku, kana an maido da tsarin yin rigakafin yaduwar cututtuka, kuma ana gudanar da wasu ayyuka yadda ya kamata ciki hadda yin allular rigakafi, sa ido kan samar da ruwan sha mai tsabta, kashe kwayoyin cuta da dai sauransu.

Haka kuma, an maido da kiwon lafiya a wurin, tare da biyan bukatun jama'a na samun jiyya kamar yadda aka saba.

An ba da labari cewa, ya zuwa karfe 5 na maraice a wannan rana, yawan mutane masu rauni da suka samu jiyya a asibiti ya kai 1254 a lardin Sichuan, inda daga cikinsu 47 sukeda mumunan rauni.

Ya zuwa yanzu dai, babu alamun yaduwar manyan cututtuka ko matsaloli na ba zato ba tsamani dangane da aikin kiwon lafiya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China