Li Keqiang ya bayyana a gun taron cewa, ya kamata a ci gaba da bada ceto ga mutanen da suka gamu da bala'in, da tsugunar da jama'ar dake fama da bala'in, bada kudin taimako ga jama'a, tabbatar da samar da gidajen kwana, abinci, ruwa ga mutane dake yankin, kara sa lura kan aikin kiwon lafiya, dawo da harkokin rayuwar jama'a a yankin da kuma kaddamar da aikin sake gina yankin cikin lokaci. (Zainab)