in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da aikin ceto a garin Lushan
2013-04-24 20:15:05 cri

An shiga kwana na biyar bayan abkuwar girgizar kasa a garin Lushan dake lardin Sichuan na kasar Sin, kuma an wuce lokacin mafi kyau na ceton mutanen da suka gamu da bala'in, amma ana ci gaba da aikin ceto a yankin.

Rukunin bada ceto ya kara gudanar da ayyukan bada ceto a yanki mai fama da bala'in, inda aka kai kayayyakin taimako ga wurare masu fama da bala'in ya shafa sosai ta hanyar jiragen sama masu saukar ungulu.

Bisa labarin da ma'aikatar kula da harkokin jama'ar kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa karfe 9 na safiyar ranar 24 ga wata, an kai tantuna dubu 47, barguna dubu 199, tufaffi dubu 10, gadahen kwanciya dubu 10 da dai sauran kayayyakin taimako zuwa yankin Lushan mai fama da bala'in.

Masana yaduwar cututtuka na kasar Sin sun bayyana cewa, akwai yiwuwar samun yaduwar cututtuka a yanki mai fama da bala'in, don haka, kamata ya yi masu bada ceto da jama'ar dake yankin sun sa lura sosai kan magance wadannan cututtuka, musamman ciwon ciki da hanyar numfashi.

Bisa labarin da aka bayar a shafin internet na hukumar kula da girgizar kasa ta kasar Sin, an ce, ya zuwa karfe 2 da rabi na yammacin ranar 24 ga wata, mutane 196 sun rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasar da ta faru a ranar 20 ga watan Afrilu a garin Lushan, mutane 21 sun bace, kana mutane 11470 sun ji rauni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China