in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya nemi a ci gaba da gudanar da aikin ceto yadda ya kamata a lardin Sichaun inda girgizar kasa ta abku
2013-04-25 15:05:34 cri

A yau Alhamis 25 ga wata, ita rana ta shida da aka fara gudanar da aikin ceto a gundumar Lushan ta lardin Sichuan inda girgizar kasa mai karfin digiri 7 bisa ma'aunin Richter ta abku. Firaministan kasar Sin Mr. Li Keqiang ya kira zaunannen taron majalisar gudanarwa a ran 24 ga wata, inda aka tsara shirin kyautata aikin ceto da kau da bala'in, da yin iyakacin kokari don rage yawan hasarar da aka samu. A sa'i daya kuma za a ci gaba da aiki wurjanjan domin ceto mutane a dukkan wuraren da gine-gine suka ruguje a kansu.

Ya zuwa karfe 12 da tsakar rana na ranar 24 ga wata, an tura sojin 'yantar da jama'ar kasar Sin da dakaru masu dauke da makamai na kasar Sin da yawansu ya kai kimanin dubu 13, kuma an tattara sojojin farar hula kimanin 5900 domin gudanar da aikin ceto a gundumomi da kauyuka 18 ciki hadda gundumar Lushan da ta Baoxing, kuma suna ci gaba da ceto wadanda bala'in girgizar kasa ya ritsa da su, tare kuma da yin iyakacin kokarin ba da jiyya ga wadanda suka ji rauni, sannan da ba da taimako wajen tsugunar da fararen hula da shiga aikin ceto.

A wannan rana kuma, an gyara hanyoyin da suka lalace saboda girgizar kasa, ta yadda za a samu tabbaci ga yin sufurin kayayyakin agaji don yin ceto da kau da bala'in.

Ban da haka, gwamnatin lardin Sichuan ya kira wani taron manema labaru cewa, makarantu 355 na birnin Ya'an sun lalace cikin hadarin, ya zuwa yanzu, wasu makarantu sun maido da karatunsu a wurin ko kuma wani wuri na daban, dadin dadawa, ana kuma sa ran cewa za a maido da ayyukan makarantu midil da firamare daga dukan fannoni daga ranar 27 ga wata.

Hukumar kula da ayyukan girgizar kasa ta kasar Sin ta ba da labari cewa, ya zuwa karfe 2 da rabi na maraicen ranar 24 ga wata, yawan mutane da suka mutu sakamakon hadarin ya kai 196, yayin da 21 suka bace kuma 11,470 suka raunana. Ban da haka, ya zuwa karfe 8 na safiyar yau Alhamis 25 ga wata, an samu kananan girgizar kasa har sau 4551. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China