in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya umurci a tsugunar da wadanda girgizar kasa ta shafa yadda ya kamata
2013-04-25 20:16:56 cri
Kwanan baya, Xi Jinping, shugaban kasar Sin ya ba da muhimmin umurni kan yadda za a yi rigakafin abkuwar bala'un da ke da nasaba da yanayin kasa da su kan biyo bayan girgizar kasa da ta faru a gundumar Lushan ta lardin Sichuan

Shugaba Xi ya bukaci hukumar lardin na Sichuan da hukumomi masu ruwa da tsaki da su ci gaba da ceton mutane, ba wa wadanda suka jikkata jinya, da tsugunar da masu fama da bala'in yadda ya kamata, a sai daya kuma su hanzarta kimanta yiwuwar abkuwar bala'un da ke da nasaba da yanayin kasa da su kan biyo bayan girgizar kasa, da barnar da bala'un za su haddasa, a kokarin hana abkuwar irin wannan bala'i.

A 'yan kwanakin nan, bisa goyon baya daga ma'aikatar kula da yankunan kasa da albarkatun kasar Sin da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki, hukumar lardin Sichuan ta aika da masana da dama zuwa yankunan da girgizar kasar ta fi yin illa, inda suka yi bincike kan wuraren da ke fuskantar barazanar abkuwar bala'un da ke da nasaba da yanayin kasa da su kan biyo bayan girgizar kasa, tare da kimanta barnar da girgizar kasar ta haddasa, a kokarin ba da gargadi kafin abkuwar bala'un cikin lokaci.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China