Ya zuwa yanzu, ana kwashe kwanaki biyar aka gudanar da aikin ceto a gundumar Lushan ta lardin Sichuan inda ake fama da girgizar kasa mai karfin maki 7 bisa ma'aunin Richter da ta abku a ran 20 ga wata, ko da yake lokacin mafi kyau wajen yin aikin ceto na bayan sa'o'i 72 da abkuwar girgizar ya wuce, amma har yanzu masu aikin ceto suna nan suna dukufa kan aikinsu na ceton mutane.
Shugaban rukunin aikin ceton mutanen da girgizar kasar ta ritsa da su na kasar Fu Xiaoguang ya nuna cewa, za su yi iyakacin kokarin ceton dukkan mutanen da suke raye a karkashin baraguzan gine-gine. A sa'i daya kuma, za su gaggauta aikin sufurin kayayyakin tallafi, gina gidajen wucin gadi, ba da tabbaci ga kiwon lafiya da aikin kwana-kwana.
Ban da haka, asibitoci daban-daban a lardin suna gayyar kokari don ba da kulawa ga wadanda suka raunana.
An ba da labari cewa, kasashen duniya na zura ido sosai kan halin da ake ciki a wuraren dake fama da bala'in girgizar kasa, tare kuma da darajanta ayyukan da gwamnati da hukumomi masu zaman kansu suka yi na yin aikin ceto.
Bisa labarin da cibiyar ba da jagoranci kan halin ko ta kwana ta gwamnatin jama'ar lardin Sichuan ta bayar, an ce, ya zuwa karfe 6 na maraice na ran 23 ga wata, adadin mutanen da suka mutu ya kai 193, yayin da 25 suka bace, wadanda suka ji rauni ya kai 12211, daga cikinsu 995 sun samu mumunan rauni.
Dadin dadawa, hukumar kula da bala'in girgizar kasa ta lardin Sichuan ta ba da labari cewa, ya zuwa karfe 8 na dare na ranar 23, an samu kananan girgizar kasa ta bi-baya har sau 3667. (Amina)