Mataimakin shugaban lardin Sichuan Zhong Mian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka yi a ranar Alhamis 25 ga wata cewa, har ila yau aikin ceto da ba da jiyya ga wadanda bala'in ya galabaitar da su, wani muhimmin aiki ne cikin wani lokaci a nan gaba. Ba shakka za a dudduba sosai a duk wuraren da gine-gine suka ruguje domin ceto mutane.
Ya zuwa yanzu, ba'a samu yaduwar cututtuka a wurin ba, kuma ana daidaita batun kiwon lafiya yadda ya kamata. Sannan an yi kokarin samar da ruwan sha mai tsabta ga mazaunan wurin.
Firaministan kasar Kazakhstan Serik Akhmetov, da firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu da dai sauran shugabannin kasa da kasa sun buga wayar tarho ko aiko da wasiku ga shugabannin kasar Sin domin nuna juyayi da boyon baya ga gwamnati da jama'ar kasar Sin game da wannan batu.
Ya zuwa karfe 6 da maraice na ran 24 ga wata, yawan mutane da suka rasa rayukansu sabo da bala'in ya kai 196, sannan 21 sun bace, kuma wasu 13,484 sun samu rauni. (Amina)