Safiyar yau Asabar 27 ga wata, an yi zaman makoki a gundumar Lushan ta lardin Sichuan inda girgizar kasa mai tsanani ya auku domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka rasa rayukansu cikin girgizar kasa, mutane kimanin 140 sun halarci bikin, ciki hadda jami'an kwamitin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na lardin Sichuan da na gwamnatin lardin da kuma na yankin soja na Chengdu har ma da mutane da suka tsira da rayukansu a yayin bala'in da sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin, jami'an tsaro na matakai daban daban, masu aikin jiyya, masu aikin ceto da masu sa kai da dai sauransu.
Masu aikin ceto da suka halarci bikin sun shedawa manema labaru cewa, za su ci gaba da yi iyakacin kokari ceton mutane da sake raya birnin Ya'an. Mutanen da bala'in ya ritsa da su kuwa, sun nuna cewa, taimakon da al'umma ta bayar ya karfafawa musu gwiwa wajen sake gina muhallinsu. (Amina)