in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lardin Sichuan zai yi zaman makoki a gobe Asabar 27 ga wata
2013-04-26 16:15:23 cri

Yau Jumma'a 26 ga wata ya zama mako daya da bala'in girgizar kasa mai tsanani mai karfin digiri 7 bisa na'aunin Ritcher ya abku a gundumar Lushan na lardin Sichuan na kasar Sin. Domin nuna ta'aziyya ga wadanda suka rasa rayukansu cikin bala'in. Gwamantin lardin Sichuan ya yanke shawarar mai da gobe ranar Asabar 27 ga wata da ta zama ranar zaman makoki a lardin.

Daga safiyar ranar Asabar 27 ga wata, za a dakatar da duk wasu shagulgula a lardin, kuma daga karfe 8 da minci 2 na safe, dukkanin jama'ar Sichuan za su yi tsit har tsawon mintoci 3 don nuna alhini, kuma a wannan lokaci dukkanin motoci, jiragen ruwa za su kada kararrawa baki daya, kuma na'urorin tsaron sararin sama za su yi karar jiniya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China