Kasashe shida da batun nukiliya na kasar Iran ya shafa suna fatan za a samu ci gaba a shawarwarin da ake yi a Alma-ata
Michael Mann, kakakin babbar wakiliyar kungiyar EU mai kula da harkokin diplomasiyya da manufofin tsaro Catherine Ashton ya bayyana a ranar 26 ga wata cewa, kasashe shida da batun nukiliya na kasar Iran ya shafa wato Amurka, Ingila, Faransa, Jamus, Rasha da kuma Sin sun yi fatan za a samu ci gaba a shawarwarin da ake yi a Alma-ata dake kasar Kazakhstan.
Mr Mann ya bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka gudanar a yayin da ake yin shawarwari kan batun nukiliya na kasar Iran a Alma-ata.
Hakazalika Mann ya nuna cewa, akwai sauran tafiya wajen warware batun nukiliya na kasar Iran. (Zainab)