Kiir ya nuna murna da yadda aka gudanar da taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 cikin nasara da kuma zabar sabbin shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da yadda aka zabi Xi Jinping a matsayin sabon babban sakataren jam'iyyar, kana ya jaddada cewa, kasar Sudan ta kudu tana son koyon fasahohin da Sin ta samu wajen raya kasa, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin a fannonin tattalin arziki, cinikayya, kayayyakin more rayuwa, bada ilmi, al'adu, kiwon lafiya da dai sauransu, kana tana fatan kasar Sin za ta kara taimaka mata da ba ta goyon baya. Kiir ya ce, jam'iyyar 'yantar da jama'ar Sudan ta dora muhimmanci kan inganta dangantakar dake tsakaninta da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana tana fatan jam'iyyun biyu za su zurfafa dangantakar dake tsakaninsu, da yin maraba da kungiyoyin Sin masu zaman kansu da su gudanar da ayyukan kyautata zaman rayuwar jama'ar Sudan ta Kudu.
A nasa bangaren, Li Jinjun ya bayyana cewa, burin ziyarar tawagarsa a kasar Sudan ta Kudu shi ne aiwatar da ayyukan da memban hukumar harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwmainis ta kasar Sin Li Yuanchao da shugabannin kasar Sudan ta kudu suka tsara yayin da Mista Li ke ziyara a Sudan ta Kudu a farkon shekarar bana. Ya ce, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, gwamnatin kasar da kuma jama'arta sun dora muhimmanci kan inganta dangantakar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Sudan ta Kudu, yana fatan za a kara yin mu'amala a tsakanin jam'iyyun biyu, da inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 da sada zumunta a tsakanin jama'arsu. (Zainab)