Bisa labarin da aka bayar, an ce, bisa kuskure ne sojojin kasar Sudan ta Kudu suka harbo wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojojin kiyaye lafiya na MDD, abun da yayi sanadiyyar mutuwar dukkan ma'aikatan jirgin hudu. Sai dai madam Hua ta ce, babu basine a cikin mamatan.
Madam Hua ta kara da cewa, an tattauna wannan lamari a gun kwamitin sulhun MDD, kuma kasar Sin ta nemi bangarori daban-daban da su gaggauta gudanar da bincike kan wannan lamari, da daukar matakan da suka wajaba don kaucema aukuwar irinsa nan gaba, da tabbatar da zaman lafiyar sojoji masu shimfida zaman lafiya.(Murtala)