Wang ya yi furucin ne yayin da yake ganawa da wasu manyan jami'an jam'iyyar 'yantar da jama'ar Sudan ta kasar Sudan ta Kudu, wadanda ke halartar wani kwas din karawa juna sani a nan kasar Sin, a karkashin jagorancin Mark Nyipuoch Ubong, mamban hukumar siyasar kasar Sudan ta Kudu, kuma shugaban kwamitin 'yan majalisun kasar.
A cewar Mista Wang, kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suka fara kulla huldar diplomasiyya tare da Sudan ta Kudu, inda kasashen 2 suka sada zumunta sosai a shekara 1 da ta gabata. Irin hadin gwiwar da ake yi a tsakanin kasashen 2 ya dace da moriyar jama'arsu, kana yana amfanawa kokarin tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba a yankin da kasar Sudan ta Kudu ke ciki. Kasar Sin tana godiya kan yadda Sudan ta Kudu ta tsaya kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, kana tana rufa wa Sudan ta Kudu baya kan kokarinta a fannonin raya tattalin arziki, kyautata zaman rayuwar jama'a, tabbatar da kwanciyar hankali, da neman shiga tsarin gamayyar kasa da kasa. Wang ya kara da cewa, kasar Sin na son yin kokari tare da Sudan ta Kudu, don kara amincewa da juna a fannin siyasa, da habaka mu'amala zuwa bangarori daban daban, da kara hadin kai, ta yadda za a iya ciyar da huldar dake tsakaninsu gaba.
A nasa bangare, Mista Mark Nyipuoch Ubong ya ce jam'iyyar 'yantar da jama'ar Sudan na son koyon fasahar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a fannin jagorar jama'a wajen raya kasa, kana ya bayyana fatansa na ganin kasashen 2 sun zurfafa hadin kansu a fannoni daban daban. (Bello Wang)