Wakilin kawancen kungiyoyin da ke adawa da gwamnatin kasar Sham wato SNCO dake birnin Paris ya nuna a ran 31 ga watan Janairu da cewa, SNCO na shirin yin shawarwari da wakilan gwmnatin ta yadda za a fito da hanyar da ta dace wajen warware rikicin kasar.
Wakilin ya shedawa manema labaru na wani gidan talabijin kasar Faransa cewa, SNCO na shirin yin shawarwari da wakilan gwamnatin kasar Sham, amma ba za su yarda da shugaban kasar Bashar al-Assad ya shiga shawarwari ba balle magoyansa. Bashar al-Assad zai iya ba da izni ga sauran jami'an gwamnatin. Ban da haka, ya yi kira ga kasashen kungiyar tarayyar Turai wato EU da su goyi bayan kungiyoyin adawa da kuma kau da takunkumi da aka garkama musu na yin sufurin makamai. (Amina)