in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron kasar Isra'ila ya yi habaici cewa, kasarsa ita ce ta kai hari kasar Sham ta sama
2013-02-05 10:41:17 cri
Ministan tsaron kasar Isra'ila Ehud Barak ya yi habaici a ran 3 ga wata kan harin da aka kaiwa kasar Sham a mako da ya gabata cewa, Isra'ila ce ta kai wannan hari.

Wannan dai shi ne Karon farko, da mahukuntan Isra'ila suka mai da martani kan wannan batu.

Yayin wani taron tsaron kasar da aka yi a birnin Munich na kasar Jamus a wannan rana, Ehud Barak ya nuna cewa, farmakin da aka kai wa sansanin soja na kasar Sahm daga sama ya bayyana cewa, kasar Isra'ila ta shiga tsanaki kan batun sanarwar da ta bayar a baya, ta hana sufurin manyan makamai zuwa kasar Lebanon.

Game da wannan batu, tuni gwamnatin kasar Sham ta zargi Isra'ila da kai hari kan wata cibiyar nazarin aikin soja dake kusa da birnin Damascus, hedkwatar kasar ta Sham a ranar Larabar makon da ya gabata. Kafin wannan karo, Isra'ila ba ta bayyana matsayinta kan wannan batu ba.

A wannan rana kuma, shugaban kasar Sham Bashar al-Assad ya nunawa sakataren kwamitin koli na tsaron kasar Iran Saeed Jalili, wanda ya kai ziyara a kasar sa cewa, kasar Sham na da karfin matuka, wajen mayar da martani ga harin da aka kai mata, tare kuma da yin Allah-wadai da matakin da Isra'ila ta dauka, saboda illar hakan ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Sham.

A nasa bangare, Saeed Jalili ya nanata cewa, Iran tana cikakken goyon bayanta ga jama'ar kasar Sham don tinkarar harin da Isra'ila ta kai mata, ya kuma bayyana cewa, Iran za ta ba da taimako ga kasar Sham wajen dakile makarkashiyar da aka shirya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China