in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara samun ci gaba dangane da warware rikicin kasar Sham, in ji ministan harkokin wajen kasar Rasha
2013-02-20 13:23:25 cri

Ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergei Lavrov, ya sanar a ranar Talata 19 ga wata cewa, kasarsa na ganin an fara kawar da halin kila-wa-kila da ake ciki dangane da warware rikicin kasar Sham.

Yayin da Sergei Lavrov ke ganawa da manema labaru a wannan rana, ya ce, Rasha na jiran ziyarar da ministan harkokin wajen kasar ta Sham zai kawo mata a ran 25 ga wata, inda bangarorin biyu za su tattauna kan matsalolin da tilas ne a warware su, idan dai ana fatan cimma nasarar shawarwari tsakanin gwamnati da 'yan adawar kasar, tare kuma da dakatar da jin karar makamai. Bugu da kari Sergei Lavrov ya ce, kasar Rasha na kokarin tuntubar wakilan 'yan adawar.

Lavrov ya ce, ba da jimawa ba, Rasha ta yi kira ga gwamnati, da 'yan adawar kasar ta Sham, da su gudanar da shawarwari ba tare da wani jinkiri ba, sai dai kungiyar adawar Syrian ta gabatar da saukar shugaba Bashar Al-Assad a matsayin sharadinta dangane da fara shawarwari. Amma kawo yanzu, 'yan adawar ba su sake gabatar da wannan sharadi ba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China